19 Saboda maganan nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa.
20 Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?”
21 Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”
22 Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima,
23 damuna ce kuma, Yesu kuwa na zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali,
24 sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.”
25 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata.