2 Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne.
3 Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari murya tasa, yakan kama sunan nasa tumaki, ya kai su waje.
4 Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye da shi, domin sun san murya tasa.
5 Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.”
6 Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.
7 Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.
8 Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, 'yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba.