33 Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.”
34 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari'arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?
35 To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi),
36 kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’?
37 In ba ayyukan da Ubana yake yi nake yi ba, to, kada ku gaskata ni.
38 Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.”
39 Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.