38 Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.”
39 Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.
40 Sa'an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can,
41 mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu'ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”
42 Nan fa mutane da yawa suka gaskata da shi.