40 “Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu,Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci,Har su juyo gare ni in warkar da su.”
41 Ishaya ya faɗi haka saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa.
42 Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a.
43 Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane da girmamawar Allah.
44 Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Wanda yake gaskatawa da ni, ba da ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.
45 Wanda kuma yake dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne.
46 Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu.