13 Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake.
14 Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna.
15 Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku
16 Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi.
17 In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne.
18 Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’
19 Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi.