1 “Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi.
2 Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.
3 Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku.
4 Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina.
5 Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba.