1 “Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe.
2 Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi.
3 Za su yi haka ne kuwa domin ba su san Uba ko ni ba.
4 Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”“Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku.