6 Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku.
7 Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.
8 Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.
9 Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba,
10 a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba.
11 a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.
12 “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba.