8 Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.
9 Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba,
10 a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba.
11 a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.
12 “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba.
13 Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku.
14 Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.