4 Duka biyu suka ruga a guje, amma almajirin nan ya tsere wa Bitrus, ya riga isa kabarin.
5 Yana duƙawa yana leƙa ciki, sai ya ga likkafanin lilin a ajiye, amma fa bai shiga ba.
6 Sa'an nan Bitrus ya zo a bayansa, ya kuwa shiga kabarin, ya ga likkafanin a ajiye,
7 mayanin kuma da yake kansa ba a ajiye tare da likkafanin yake ba, amma a naɗe shi kaɗai a waje ɗaya.
8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga, ya gani, ya kuma ba da gaskiya.
9 Don kafin lokacin nan ba su fahimci Nassin nan ba, cewa lalle ne yă tashi daga matattu.
10 Sai almajiran suka koma gida.