9 Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?”
10 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba?
11 Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu.
12 In na yi muku zancen al'amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al'amuran sama?
13 Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum da yake Sama.
14 Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,
15 domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.