1 Bayan haka aka yi wani idi na Yahudawa, Yesu kuwa ya tafi Urushalima.
2 A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da ake ce da shi Betasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar.
3 A shirayin nan kuwa marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu. [Suna jira a motsa ruwan.
4 Don lokaci lokaci wani mala'ika yakan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan an motsa ruwan, sai ya warke daga duk irin cutar da yake da ita.]