20 Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al'ajabi.
21 Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa.
22 Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan,
23 domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.
24 Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.
25 “Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu.
26 Yadda Uba kansa yake tushen rai, haka ya sa Ɗan ya zama tushen rai.