1 Bayan haka Yesu ya haye Tekun Galili, wato Tekun Tibariya.
2 Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu'ujizan da yake yi ga marasa lafiya.
3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa.
4 To, Idin Ƙetarewa, wato idin Yahudawa, ya gabato.
5 Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?”