3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa.
4 To, Idin Ƙetarewa, wato idin Yahudawa, ya gabato.
5 Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?”
6 Ya faɗi haka ne fa domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.
7 Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.”
8 Sai Andarawas ɗan'uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa,
9 “Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”