42 Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?”
43 Sai kuma rabuwa ta shiga tsakaninsu a kansa.
44 Waɗansunsu suka so su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi.
45 Daga nan dogaran Haikali suka koma wurin manyan firistoci da Farisiyawa, su kuwa suka ce musu, “Don me ba ku kawo shi ba?”
46 Sai dogaran suka amsa suka ce, “A'a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan!”
47 Sai Farisiyawa suka amsa musu suka ce, “Af! Har ku ma an ɓad da ku ne?
48 Ashe, akwai wani daga cikin shugabanni ko Farisiyawa da ya gaskata da shi?