5 Domin ko dā ma 'yan'uwansa ba su gaskata da shi ba.
6 Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku, koyaushe lokacinku ne.
7 Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne.
8 Ku dai ku tafi idin. Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.”
9 Da ya faɗa musu haka, ya dakata a ƙasar Galili.
10 Bayan 'yan'uwansa sun tafi idin kuwa, shi ma ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba.
11 Yahudawa suna ta nemansa a wurin idin suna cewa, “Ina yake ne?”