50 Nikodimu kuwa da ya je wurinsa dā, yana kuwa ɗaya daga cikinsu, ya ce musu,
51 “Ashe, shari'armu takan hukunta mutum tun ba a ji daga bakinsa ba, an kuma san abin da yake ciki?”
52 Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.”[
53 Sai kowa ya tafi gida.