23 Aka faɗa wa sarki cewa, ga annabi Natan. Da ya zo gaban sarki, sai ya rusuna ya gaishe shi.
24 Sa'an nan ya ce, “Ranka ya daɗe, ashe, ko ka sanar, cewa Adonija ne zai gaje ka?
25 Gama yau ɗin nan ya tafi ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Yowab shugaban sojoji, da Abiyata firist. Ga shi, suna ci suna sha tare da shi, suna cewa, ‘Ran sarki Adonija ya daɗe.’
26 Amma ni da Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da ɗanka Sulemanu, bai gayyace mu ba.
27 Ranka ya daɗe ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fādawanka, cewa ga wanda zai gāje ka ba?”
28 Sai sarki Dawuda ya ce, “A kirawo mini Bat-sheba.” Ta kuwa zo gaban sarki.
29 Sa'an nan ya ce mata, “Na yi miki alkawari da Ubangiji mai rai wanda ya fanshe ni daga dukan wahala,