29 Sa'an nan ya ce mata, “Na yi miki alkawari da Ubangiji mai rai wanda ya fanshe ni daga dukan wahala,
30 a yau ne kuma zan cika alkawarin da na yi miki da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, cewa Sulemanu, ɗanki, zai yi mulki a bayana, shi ne zai hau gadon sarautata ya gāje ni, haka kuwa zan yi yau.”
31 Bat-sheba kuwa ta rusuna har ƙasa, domin girmamawa, ta ce, “Ran ubangijina sarki ya daɗe har abada!”
32 Sarki Dawuda kuma ya ce, “Ku kirawo mini Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada.” Su kuwa suka zo gaban sarki,
33 ya ce musu, “Ku tafi tare da fādawana, ku sa Sulemanu, ɗana, ya hau alfadarina, ku kai shi Gihon,
34 a can Zadok firist, da annabi Natan za su zuba masa mai, ya zama sarkin Isra'ila, sa'an nan ku busa ƙaho, ku ce, ‘Ran sarki Sulemanu ya daɗe.’
35 Sa'an nan ku zo da shi ya hau gadon sarautata, gama shi ne zai zama sarki a maimakona. Na sa shi ya zama mai mulkin Isra'ila da Yahuza.”