1 Sarauniyar Sheba ta ji labarin sunan da Sulemanu ya yi ta dalilin sunan Ubangiji, ta zo don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya.
2 Ta iso Urushalima da 'yan rakiya da yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya da yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa duk abin da yake a ranta.
3 Sulemanu ya amsa tambayoyinta dukka, ba abin da ya gagare shi amsawa.
4-5 Sarauniyar Sheba ta yi mamaki sa'ad da ta ga hikimar Sulemanu, da gidan da ya gina, da irin abincinsa, da irin zaman fādawansa, da yadda ma'aikatan gida suke hidima, da irin tufafinsu, da masu ba da abin sha, da hadayu na ƙonawa waɗanda yakan miƙa cikin Haikalin Ubangiji.