21 Da Rehobowam ya komo Urushalima, sai ya tara dukan jama'ar gidan Yahuza, da na kabilar Biliyaminu. Aka sami mayaƙa dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) waɗanda za su yi yaƙi da gidan Isra'ila, don su komar da su a ƙarƙashin mulkin Rehobowam, ɗan Sulemanu.