30 Wannan abu ya zama zunubi, gama mutane sun tafi wurin siffofin maruƙan nan a Betel da Dan.
31 Ya kuma gina masujadai a tuddai, sa'an nan ya sa waɗansu daga cikin mutane waɗanda ba Lawiyawa ba, su zama firistoci.
32 Yerobowam kuma ya sa a yi idi ran goma sha biyar ga wata na takwas kamar yadda ake yi a Yahuza. Ya miƙa hadayu bisa bagade, haka ya yi a Betel. Ya yi ta miƙa hadayu ga siffofin maruƙan da ya yi. Ya kuma sa firistoci a masujadan da ya gina a Betel.
33 Ya tafi gaban bagaden da ya gina a Betel a rana ta goma sha biyar ga wata na takwas, wato watan da ya zaɓa don kansa. Ya kafa wa jama'ar Isra'ila idi. Sai ya tafi don ya ƙona turare a kan bagaden.