1 A lokacin nan Abaija ɗan Yerobowam ya kwanta ciwo.
2 Yerobowam kuwa ya ce wa matarsa, “Ki tashi, ki ɓad da kama don kada a sani ke matata ce, sa'an nan ki tafi Shilo wurin Ahija, annabin nan wanda ya ce mini zan sarauci jama'an nan.
3 Ki ɗauki malmalar abinci guda goma, da waina, da kurtun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.”
4 Matar kuwa ta yi haka. Ta tashi ta tafi Shilo a gidan Ahija. Ahija ba ya gani, saboda tsufa.