31 Da yake abu ne mai sauƙi a gare shi ya bi hanyar zunuban Yerobowam ɗan Nebat, sai ya auro Yezebel 'yar Etba'al, Sarkin Sidon, ya kuma bauta wa gunkin nan Ba'al, ya yi masa sujada.
32 Ya gina wa Ba'al bagade a matsafar Ba'al ɗin, da ya gina a Samariya.
33 Ahab kuma ya yi gunkiyan nan Ashtoret. Ahab dai ya yi abin da ya sa Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra'ila waɗanda suka riga shi.
34 A cikin kwanakinsa, Hiyel mutumin Betel ya gina Yariko. Ya yi hasarar ɗan farinsa, Abiram, sa'ad da ya kafa harsashin ginin, ya kuma yi hasarar autansa, Segub, sa'ad da ya sa ƙofofin, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Joshuwa ɗan Nun.