43 To, me ya sa ka karya rantsuwar da ka yi da sunan Ubangiji, da kuma umarnin da na umarce ka?”
44 Sarki kuma ya ce masa, “Ka sani sarai irin duk muguntar da ka yi wa tsohona, Dawuda. Haka kuma Ubangiji zai sāka maka bisa ga muguntarka.
45 Amma Ubangiji zai sa mini albarka, ya kuma tabbatar da gadon sarautar Dawuda har abada.”
46 Sa'an nan sarki ya umarci Benaiya ɗan Yehoyada, ya tafi, ya kashe Shimai. Yanzu sarauta ta tabbata a hannun Sulemanu.