1 Da Sulemanu ya gama ginin Haikalin Ubangiji da na fāda, da dukan abin da ya so ya yi,
2 sai Ubangiji ya sāke bayyana gare shi, kamar yadda ya bayyana gare shi a Gibeyon.
3 Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu'arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum.
4 Amma kai, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda tsohonka, Dawuda, ya yi da aminci, da sahihanci, kana aikata dukan abin da na umarce ka, kana kuma kiyaye dokokina da ka'idodina,
5 sa'an nan zan kafa gadon sarautarka a bisa Isra'ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa tsohonka, Dawuda, sa'ad da na ce masa ba za a rasa mutum daga zuriyarsa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.