1 Da Sulemanu ya gama ginin Haikalin Ubangiji da na fāda, da dukan abin da ya so ya yi,
2 sai Ubangiji ya sāke bayyana gare shi, kamar yadda ya bayyana gare shi a Gibeyon.
3 Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu'arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum.
4 Amma kai, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda tsohonka, Dawuda, ya yi da aminci, da sahihanci, kana aikata dukan abin da na umarce ka, kana kuma kiyaye dokokina da ka'idodina,
5 sa'an nan zan kafa gadon sarautarka a bisa Isra'ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa tsohonka, Dawuda, sa'ad da na ce masa ba za a rasa mutum daga zuriyarsa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.
6 Amma idan kai, ko 'ya'yanka, kun bar bina, ba ku kiyaye umarnaina da dokokina ba, waɗanda na yi muku, amma kuka tafi, kuka bauta wa waɗansu gumaka, kuka yi musu sujada,