26 Reyu ya haifi Serug, Serug ya haifi Nahor, Nahor ya haifi Tera,
27 Tera ya haifi Abram, wato Ibrahim ke nan.
28 'Ya'yan Ibrahim, maza, su ne Ishaku da Isma'ilu.
29 Ga zuriyarsu. Nabayot shi ne ɗan farin Isma'ilu, sa'an nan sai Kedar, da Abdeyel, da Mibsam,
30 da Mishma, da Duma, da Massa, da Hadad, da Tema,
31 da Yetur, da Nafish, da Kedema. Waɗannan su ne 'ya'yan Isma'ilu, maza.
32 'Ya'ya maza na Ketura, wato ƙwarƙwarar Ibrahim, su ne Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. 'Ya'yan Yokshan, maza, su ne Sheba, da Dedan.