1 Dukan Isra'ilawa kuwa suka taru wurin Dawuda a Hebron, suka ce masa, “Mu ɗaya ne da kai.
2 Ko dā can lokacin da Saul yake sarauta, kai ne kake yi wa Isra'ilawa jagora zuwa yaƙi da komowa. Ubangiji Allahnka kuwa ya ce maka, ‘Za ka yi kiwon jama'ata, wato Isra'ilawa, ka kuma shugabance su.’ ”
3 Sai dattawan Isra'ilawa suka zo wurin sarki Dawuda a Hebron. Dawuda kuwa ya yi alkawari da su a Hebron a gaban Ubangiji, ake kuwa naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila bisa ga faɗar Ubangiji ta bakin Sama'ila.
4 Sarki Dawuda kuwa, tare da dukan Isra'ilawa, suka tafi Urushalima, wato Yebus inda Yebusiyawa suke zaune.