1 Tar 11:20-26-47 HAU

20 Abishai ɗan'uwan Yowab kuwa shi ne shugaban jarumawa talatin ɗin. Ya girgiza mashinsa, ya kashe mutum ɗari uku. Ya yi suna a cikin jarumawan nan talatin.

21 Cikin jarumawa talatin ɗin, shi ya shahara har ya zama shugabansu. Amma duk da haka bai kai ga jarumawan nan uku ba.

22 Benaiya ɗan Yehoyada, ɗan wani jarumi ne daga Kabzeyel, ya yi manyan ayyuka, ya kashe jarumawa biyu na Mowabawa. Sai ya gangara ya kashe zaki a cikin rami a ranar da ake yin dusar ƙanƙara.

23 Sai kuma ya kashe wani dogon Bamasare mai tsayi kamu biyar. Bamasaren yana da māshi mai kama da dirkar masaƙa a hannunsa, amma sai ya gangaro wurinsa da kulki a hannu, ya ƙwace māshin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da shi.

24 Waɗannan abubuwa Benaiya ɗan Yehoyada ya yi su, ya kuwa yi suna kamar manyan jarumawan nan uku.

25 Ya yi suna a cikin jarumawa talatin ɗin, amma bai kai ga jarumawan nan uku ba. Sai Dawuda ya sa shi ya zama shugaban matsaransa.

26-47 Waɗannan su ne manyan jarumawan sojoji.Asahel ɗan'uwan YowabElhanan ɗan Dodo daga BaitalamiShamma daga HarodHelez daga FeletAira ɗan Ikkesha daga TekowaAbiyezer daga AnatotSibbekai daga HushaIlai daga AhoMaharai daga NetofaHeled ɗan Ba'ana daga NetofaIttayi ɗan Ribai daga Gibeya ta BiliyaminuBenaiya na FiratonHurai daga rafuffuka kusa da Ga'ashAbiyel daga ArabaAzmawet daga BahurimEliyaba daga Shalim'Ya'yan Yashen, maza, daga GizonJonatan ɗan Shimeya daga HarodAhiyam ɗan Sharar daga HarodElifelet ɗan AhasbaiHefer daga MekaraAhaija daga FeletHezro daga KarmelNayarai ɗan EzbaiYowel ɗan'uwan NatanMibhar ɗan HagriZelek daga AmmonNaharai daga Biyerot (Mai riƙe wa Yowab ɗan Zeruya makamai)Aira da Gareb daga YattirUriya BahitteZabad ɗan AlaiAdina ɗan Shiza (Shi ne shugaba a kabilar Ra'ubainu, yana da ƙungiyarsa mai soja talatin tare da shi)Hanan ɗan Ma'akaYoshafat daga MitnaUzziya daga AshteraShama da Yehiyel 'ya'yan Hotam, maza, daga ArowerYediyel da Yoha 'ya'yan Shimri, maza, daga TizEliyel daga MahawaYeribai, da Yoshawiya 'ya'yan Elna'am, mazaItma daga MowabEliyel, da Obida, da Yawasiyel daga Zoba,