7 Sa'an nan Dawuda ya zauna a kagara, don haka aka kira birnin, birnin Dawuda.
8 Sai ya rutsa birnin da gini tun daga Millo. Yowab kuma ya gyaggyara sauran birnin.
9 Dawuda ya yi ta ƙasaita gaba gaba saboda Ubangiji Mai Runduna yana tare da shi.
10 Waɗannan su ne shugabanni, wato manyan jarumawan Dawuda waɗanda suka goyi bayansa sosai a mulkinsa, tare da dukan Isra'ilawa waɗanda suka naɗa shi sarki bisa ga maganar Ubangiji a kan Isra'ilawa.
11 Wannan shi ne labarin manyan jarumawan Dawuda. Yashobeyam ɗan Bahakmone shi ne shugaban jarumawa talatin. Ya karkashe mutum ɗari uku da māshinsa baki ɗaya.
12 Na biye da shi shi ne Ele'azara ɗan Dodo, Ba'ahohiye, wanda yake ɗaya daga cikin manyan jarumawan nan uku.
13 Yana tare da Dawuda a Efes-dammin sa'ad da Filistiyawa suka taru wuri ɗaya don su yi yaƙi. Akwai wata gonar sha'ir a wurin, sai jama'a suka gudu daga gaban Filistiyawa.