8 Waɗannan su ne sunayen shahararru, ƙwararrun mayaƙa daga kabilar Gad, waɗanda suka haɗa kai da sojojin Dawuda, sa'ad da yake a kagara a hamada. Su gwanayen yaƙi da garkuwa da mashi ne. Fuskokinsu kamar na zakoki, saurinsu kamar bareyi a kan dutse.
9-13 Ga yadda aka lasafta su bisa ga matsayinsu, da Ezer, da Obadiya, da Eliyab, da Mishmanna, da Irmiya, da Attai, da Eliyel, da Yohenan, da Elzabad, da Irmiya, da Makbannai.
14 Waɗannan daga kabilar Gad shugabannin sojoji ne, waɗansu na mutum dubu, sauransu kuma ƙananan shugabanni ne waɗanda suke shugabancin sojoji ɗari.
15 Su ne waɗanda suka haye Urdun a watan fari na shekara, sa'ad da Kogin Urdun ɗin ya yi ambaliya. Suka kori waɗanda suke zaune a kwaruruka, na wajen gabas da yamma da kogin.
16 Sa'an nan waɗansu daga cikin mazajen Biliyaminu da na Yahuza, suka zo wurin Dawuda a kagararsa.
17 Sai Dawuda ya fito don ya tarye su, ya ce musu, “Idan da salama kuka zo wurina don ku taimake ni, to, zuciyata za ta zama ɗaya da taku, amma idan kun zo ne don ku bashe ni ga maƙiyana, to, Allah na kakanninmu ya duba ya shara'anta, da yake ba ni da laifi.”
18 Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Amasa wanda daga baya ya zama shugaban talatin ɗin, sai ya ce,“Muna tare da kai, ya Dawuda ɗan Yesse!Allah ya ba ka nasara tare da waɗanda suke tare da kai!Allah yana wajenka!”Sa'an nan Dawuda ya marabce su, ya maishe su shugabanni a sojojinsa.