1 Sa'an nan Dawuda ya yi shawara da shugabannin sojoji na dubu dubu da na ɗari ɗari, da kowane shugaba.
2 Ya kuma yi magana da dukan taron Isra'ilawa, ya ce, “Idan kun ga ya yi kyau, idan kuma nufin Ubangiji Allahnmu ne, to, bari mu aika a ko'ina wurin 'yan'uwanmu waɗanda aka rage a ƙasar Isra'ila, mu kuma aika wa firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a biranensu masu makiyaya domin su zo wurinmu.
3 Sa'an nan mu ɗauko akwatin alkawari na Allahnmu mu kawo shi wurinmu, gama mun ƙyale shi tun zamanin Saul.”
4 Jama'a kuwa suka amince da shawarar, suka yarda kuma a yi haka ɗin.