1 Suka fa shigo da akwatin alkawarin Allah, suka ajiye shi a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa masa, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama a gaban Allah.
2 Da Dawuda ya gama miƙa hadayar ƙonawa da ta salama, sai ya sa wa jama'a albarka da sunan Ubangiji.
3 Ya kuma rarraba wa Isra'ilawa mata da maza, gurasa, da gunduwar nama, da kauɗar zabibi.
4 Ya kuma sa waɗansu Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka Ubangiji Allah na Isra'ila, su gode masa, su kuma yabe shi.
5 Asaf shi ne shugaba, na biye da shi su ne Zakariya da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Mattitiya, da Eliyab, da Benaiya, da Obed-edom, da Yehiyel, waɗanda za su kaɗa molaye da garayu. Asaf kuwa shi ne mai kaɗa kuge.
6 Benaiya da Yahaziyel firistoci, su ne za su riƙa busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah.