41 Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya shi ne mahaifin Elishama.
42 Ɗan Kalibu, ɗan'uwan Yerameyel, shi ne Mesha ɗan farinsa wanda ya haifi Zif. Zif ya haifi Maresha wanda ya haifi Hebron.
43 'Ya'yan Hebron, maza, su ne Kora, da Taffuwa, da Rekem, da Shema.
44 Shema shi ne mahaifin Raham wanda ya kafa Yorkeyam. Rekem kuwa shi ne mahaifin Shammai.
45 Shammai shi ne mahaifin Mayon, Mayon kuwa shi ne mahaifin Bet-zur.
46 Efra ƙwarƙwarar Kalibu, ta haifi Haran, da Moza, da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.
47 'Ya'yan Yadai, maza, su ne Regem, da Yotam, da Geshan, da Felet, da Efa, da Sha'af.