7 Karmi shi ne mahaifin Akan wanda ya jawo wa Isra'ila wahala a kan abin da aka haramta.
8 Etan yana da ɗa guda ɗaya, shi ne Azariya.
9 'Ya'yan Hesruna, maza, waɗanda aka haifa masa, su ne Yerameyel, da Arama, da kuma Kalibu.
10 Arama shi ne mahaifin Amminadab. Amminadab kuma shi ne mahaifin Nashon, shugaban 'ya'yan Yahuza.
11 Nashon shi ne mahaifin Salmon. Salmon kuwa shi ne mahaifin Bo'aza.
12 Bo'aza kuma shi ne mahaifin Obida. Obida shi ne mahaifin Yesse.
13 Yesse shi ne mahaifin Eliyab ɗan farinsa, sa'an nan sai Abinadab da Shimeya,