5 Yaƙi kuma ya sake tashi tsakanin Isra'ilawa da Filistiyawa, sai Elhanan ɗan Yayir, ya kashe Lahmi ɗan'uwan Goliyat daga Gat, wanda yake gorar mashinsa ta yi ya dirkar masaƙa.
6 Yaƙi ya sāke tashi a Gat, inda wani cindo, ƙaton mutum yake. Yana da yatsotsi ashirin da huɗu, wato a kowane hannu yana da yatsa shida, haka nan kuma a kowace ƙafarsa. Shi kuma daga zuriyar ƙattin nan ne.
7 Sa'ad da ya yi wa mutanen Isra'ila ba'a, sai Jonatan ɗan Shimeya, wato ɗan'uwan Dawuda, ya kashe shi.
8 Waɗannan uku ne Dawuda da jama'arsa suka kashe daga zuriyar ƙattin na Gat.