1 Shaiɗan ya tashi gaba da Isra'ila, sai ya iza Dawuda ya ƙidaya Isra'ilawa.
2 Dawuda fa ya ce wa Yowab da sauran shugabannin jama'a, “Ku tafi, ku ƙidaya jama'ar Isra'ila tun daga Biyer-sheba har zuwa Dan, ku kawo mini labari don in san yawansu.”
3 Amma Yowab ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya yawan jama'arsa har sau ɗari bisa kan yadda suke a yanzu! Ranka ya daɗe, ya sarki, ashe, dukkansu ba naka ba ne? Me zai sa shugabana ya so a yi haka? Me zai sa ya zama sanadin tuntuɓe ga mutanen Isra'ila?”
4 Duk da haka, sarki ya sa Yowab ya bi umarninsa. Sai Yowab ya tashi, ya bibiya ƙasar Isra'ila duka, sa'an nan ya komo Urushalima.