6 Amma bai ƙidaya Lawiyawa da mutanen Biliyaminu ba, domin Yowab bai ji daɗin umarnin sarki ba.
7 Allah bai ji daɗin wannan al'amari ba, don haka sai ya bugi Isra'ila.
8 Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai saboda abin nan da na aikata. Amma ina roƙonka ka gafarta mini laifina, gama na yi aikin wauta ƙwarai da gaske.”
9 Sa'an nan Ubangiji ya yi magana da Gad, annabin Dawuda, ya ce,
10 “Je ka ka faɗa wa Dawuda, ka ce, ‘Ubangiji yana so ka zaɓi ɗaya daga cikin abu uku, wanda zai yi maka.’ ”
11 Gad kuwa ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka zaɓa,
12 ko shekara uku na yunwa, ko kuwa ka sha ɗibga a hannun maƙiyanka har wata uku, maƙiyanka su yi ta fafararka, ko kwana uku na takobin Ubangiji, wato annoba ke nan da zai aukar wa ƙasar, mala'ikan Ubangiji zai yi ta hallakarwa ko'ina a ƙasar Isra'ila. Yanzu fa, sai ka yi tunani, ka ba ni amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”