14 Amma 'ya'yan Musa mutumin Allah, an lasafta su tare da kabilar Lawi.
15 'Ya'yan Musa, maza, ke nan, Gershom da Eliyezer.
16 Ɗan Gershom babba shi ne Shebuwel.
17 Ɗan Eliyezer shi ne Rehabiya, shugaba, shi Eliyezer ba shi da waɗansu 'ya'ya, amma Rehabiya yana da 'ya'ya da yawa.
18 Ɗan Izhara shi ne Shelomit, shugaba.
19 'Ya'yan Hebron, maza, su ne Yeriya, shi ne babba, da Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da kuma Yekameyam na huɗu.
20 'Ya'yan Uzziyel, maza, su ne Mika, da Isshiya.