20 Sauran 'ya'yan Lawi, maza, na wajen Amram, shi ne Shebuwel.Na wajen Shebuwel, shi ne Yedaiya.
21 Na wajen Rehabiya, shi ne Isshiya,
22 Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.
23 Na wajen Hebron, su ne Yeriya na fari, da Amariya, da Yahaziyel, da Yekameyam.
24 Na wajen Uzziyel, shi ne Mika, na wajen Mika, shi ne Shamir.
25 Ɗan'uwan Mika, shi ne Isshiya. Na wajen Isshiya, shi ne Zakariya.
26 Na wajen Merari, Mali da Mushi, da Yayaziya. Na wajen Yayaziya, shi ne Beno.