1 Ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi ke nan. Na wajen Kora shi ne Shallum ɗan Kore, daga cikin iyalin Ebiyasaf.
2 Shallum kuwa yana da 'ya'ya maza, su ne Zakariya, da Yediyayel, da Zabadiya, da Yatniyel,
3 da Elam, da Yehohanan, da Eliyehoyenai, su bakwai ke nan.
4 Obed-edom kuma Allah ya ba shi 'ya'ya maza, su ne Shemaiya, da Yehozabad, da Yowa, da Sakar, da Netanel,
5 da Ammiyel, da Issaka, da Fauletai, da su Allah ya sa masa albarka.