1 Tar 27:1-23 HAU

1 Ga lissafin kawunan iyalin Isra'ilawa, da shugabannin dangi, da jama'a masu gudanar da ayyukan mulki. A kowane wata akan sauya aikin ƙungiyar mutum dubu ashirin da dubu huɗu (24,000), a ƙarƙashin shugaban aiki na wannan wata. Kowane wata akan sauya, wata ƙungiya ta kama aiki.

2-15 Waɗannan su ne shugabanni don kowane wata.Wata na 1, Yashobeyam, ɗan Zabdiyel. (Shi daga dangin Feresa na kabilar Yahuza ne.)Wata na 2, Dodai, ɗan Ahowa. (Miklot yake bi masa a shugabancin.)Wata na 3, Benaiya, ɗan Yehoyada firist. Shugaba ne daga cikin sanannun nan “talatin.” (Ɗansa Ammizzabad ya gāje shi a shugabancin ƙungiya.)Wata na 4, Asahel, ƙanen Yowab. (Ɗansa Zabadiya ya gāje shi.)Wata na 5, Shimeya, daga zuriyar Izhara.Wata na 6, Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa.Wata na 7, Helez, mutumin Ifraimu, daga Felet.Wata na 8, Sibbekai, daga garin Husha. (Shi daga dangin Zera ne, na kabilar Yahuza.)Wata na 9, Abiyezer, daga Anatot na kabilar Biliyaminu.Wata na 10, Maharai, daga Netofa. (Shi ma daga dangin Zera ya fito.)Wata na 11, Benaiya, daga Firaton na kabilar Ifraimu.Wata na 12, Heled, daga Netofa. (Shi daga zuriyar Otniyel ne.)

16-22 Ga jerin sunayen masu mulkin kabilan Isra'ila. Ra'ubainu: Eliyezer ɗan Zikri, Saminu: Shefatiya ɗan Ma'aka, Lawi: Hashabiya ɗan Kemuwel, Haruna: Zadok, Yahuza: Eliyab ɗaya daga cikin 'yan'uwan sarki Dawuda, Issaka: Omri ɗan Maikel, Zabaluna: Ishmaiya ɗan Obadiya, Naftali: Yerimot ɗan Azriyel, Ifraimu: Hosheya ɗan Azaziya, Manassa ta Yamma: Yowel ɗan Fedaiya, Manassa ta Gabas: Iddo ɗan Zakariya, Biliyaminu: Yawasiyel ɗan Abner, Dan: Azarel ɗan Yeroham. Waɗannan su ne shugabannin kabilai.

23 Sarki Dawuda bai ƙidaya waɗanda shekarunsu suka kasa ashirin ba, gama Ubangiji ya yi alkawari zai sa mutanen Isra'ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.