10 Ka lura, gama Ubangiji ya zaɓe ka domin ka gina Haikali, wato Wuri Mai Tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama aiki.”
11 Sa'an nan Dawuda ya ba ɗansa Sulemanu tsarin shirayin Haikalin, da ɗakunansa, da ɗakunan ajiya, da benaye, da Wuri Mafi Tsarki, inda ake gafarta zunubi.
12 Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji.
13 Ya kuma ba shi tsarin ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, da na dukan hidimar da za a yi a Haikalin Ubangiji, da aikin lura da kayayyakin aiki na cikin Haikalin Ubangiji.
14 Ya kuma faɗa wa Sulemanu yawan zinariya da za a yi kwanoni da ita don yin aiki, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita don yin aiki,
15 da yawan zinariya da za a yi alkukan fitilu, da kuma fitilun, da yawan zinariya da za a yi kowane alkuki da fitilunsa, da yawan azurfa da za a yi alkuki bisa ga yadda za a yi amfani da kowane alkuki,
16 da yawan zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa, da azurfar da za a yi teburorin azurfa,