1 'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Feresa, da Hesruna, da Karmi, da Hur, da Shobal.
2 Rewaiya ɗan Shobal, shi ne mahaifin Yahat. Yahat shi ya haifi Ahumai, da Lahad. Waɗannan su ne iyalin Zoratiyawa.
3 Waɗannan kuma su ne 'ya'yan Itam, Yezreyel, da Ishma, da Idbasha, da 'ya ɗaya, ita ce Hazzelelfoni.
4 Feniyel shi ne mahaifin Gedor, Ezer kuwa shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne 'ya'yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, zuriyarsa ne suka kafa Baitalami.