11 Kalibu ɗan'uwan Shuwa, shi ne mahaifin Mehir wanda ya haifi Eshton.
12 Eshton kuwa shi ne ya haifi Bet-rafa, da Faseya, da Tehinna wanda ya kafa birnin Ir-nahash, zuriyar waɗannan mutane kuwa su suka zauna a Reka.
13 'Ya'yan Kenaz, maza, su ne Otniyel da Seraiya. Yana kuma da waɗansu 'ya'ya maza, su ne Hatata da Meyonotai.
14 Meyonotai kuwa shi ne mahaifin Ofra.Seraiya shi ne ya haifi Yowab, Yowab ya kafa kwarin Ge-harashim, saboda su masu sana'a ne.
15 'Ya'yan Kalibu, maza, ɗan Yefunne, su ne Airu, da Ila, da Na'am. Ila shi ya haifi Kenaz.
16 'Ya'yan Yehallelel, maza, su ne Zif, da Zifa, da Tiriya, da Asarel.
17-18 'Ya'yan Ezra, maza, su ne Yeter, da Mered, da Efer, da Yalon. Bitiya 'yar Fir'auna, wadda Mered ya aura, ta haifi waɗannan, Maryamu, da Shammai, da Ishaba wanda ya haifi Eshtemowa. Mered kuma ya auri wata daga kabilar Yahuza, ta haifi Yered wanda ya kafa garin Gedor. Eber kuma ya kafa garin Soko, Yekutiyel kuwa ya kafa garin Zanowa.