21 'Ya'yan Shela, maza, ɗan Yahuza, su ne Er wanda ya kafa garin Leka, da La'ada wanda ya kafa garin Maresha, da iyalan gidan masu aikin lilin da suke zaune a Bet-ashbeya,
22 da Yokim, da mutanen da suke zaune a Kozeba, da Yowash, da Saraf, waɗanda suka yi sarauta a Mowab, sa'an nan suka zauna a Baitalami. (Waɗannan labaru na tun dā ne.)
23 Su ne maginan tukwane, waɗanda suke zaune a Netayim da Gedera. Sun zauna tare da sarki don su yi masa aiki.
24 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin, da Zohar, da Shawul,
25 da Shallum ɗansa, da Mibsam jīkansa, da Mishma jīkan ɗansa.
26 'Ya'yan Mishma, maza, su ne Hammuwel, da Zakkur, da Shimai.
27 Shimai yana da 'ya'ya maza goma sha shida, da 'ya'ya mata shida, amma 'yan'uwansa ba su da 'ya'ya da yawa kamarsa. Iyalin Saminu ba su kai yawan na Yahuza ba.