23 Su ne maginan tukwane, waɗanda suke zaune a Netayim da Gedera. Sun zauna tare da sarki don su yi masa aiki.
24 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin, da Zohar, da Shawul,
25 da Shallum ɗansa, da Mibsam jīkansa, da Mishma jīkan ɗansa.
26 'Ya'yan Mishma, maza, su ne Hammuwel, da Zakkur, da Shimai.
27 Shimai yana da 'ya'ya maza goma sha shida, da 'ya'ya mata shida, amma 'yan'uwansa ba su da 'ya'ya da yawa kamarsa. Iyalin Saminu ba su kai yawan na Yahuza ba.
28 Suka zauna a waɗannan garuruwa, wato Biyer-sheba, da Molada, da Hazar-shuwal,
29 da Bilha, da Ezem, da Eltola,